>

Abubakar Mahmoud Gumi — 207

9:123 Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yãƙi waɗanda suke kusantar[1] ku daga kãfirai. Kuma su sami tsanani daga gare ku. Kuma ku sani cẽwa Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.

9:124 Kuma idan aka saukar[1] da wata sũra, to, daga gare su akwai waɗanda suke cẽwa: "Wãne a cikinku wannan sũra ta ƙãra masa ĩmãni?" To amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma sũ, sunã yin bushãra (da ita).

9:125 Amma kuma waɗanda suke a cikin zukãtansu akwai cũta, to, tã ƙãra musu ƙazanta zuwa ga ƙazantarsu, kuma su mutu alhãlin kuwa sunã kãfirai.

9:126 Shin, bã su ganin cẽwa anã fitinar su a cikin kõwace shẽkara: Sau ɗaya kõ kuwa sau biyu, sa'an nan kuma bã su tũba, kuma ba su zama sunã tunãni ba?

9:127 "Kuma idan haƙĩƙa, aka saukar da wata sũra, sai sãshensu ya yi dũbi zuwa ga wani sãshe, (su ce): "Shin, wani mutum yanã ganin ku?" Sa'an nan kuma sai su jũya. Allah Ya jũyar da zukãtan su, dõmin, haƙĩƙa sũ mutãne ne, bã su fahimta.

9:128 Lalle ne, haƙĩƙa, Manzo[1] daga cikinku yã je muku. Abin da kuka wahala da shi mai nauyi ne a kansa. Mai kwaɗayi ne sabõda ku. Ga muminai Mai tausayi ne, Mai jin ƙai.

9:129 To, idan sun jũya, sai ka ce: Ma'ishĩna Allah ne. Bãbu abin bautãwa fãce shi. A gare Shi nake dõgara. Kuma Shi ne Ubangijin Al'arshi mai girma.