Abubakar Mahmoud Gumi — 2
2:1 A. L̃. M̃.
2:2 Wãncan ne Littãfi, bãbu shakka a cikinsa, shiriya ne ga mãsu taƙawa.[1]
2:3 Waɗanda suke yin ĩmãni game da gaibi, kuma suna tsayar da salla, kuma daga abin da Muka azurta su suna ciyarwa.
2:4 Kuma waɗanda suke yin ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabãninka, kuma game da Lãhira suna yin yaƙĩni.
2:5 Waɗancan suna kan shiriya, daga Ubangjinsu, kuma waɗannan su ne mãsu cin nasara.