>

Abubakar Mahmoud Gumi — 197

9:62 Sunã rantsuwa da Allah sabõda ku, dõmin su yardar da ku. Kuma Allah da ManzonSa ne mafi cancantar su yardar da Shi, idan sun kasance mũminai.

9:63 Shin, ba su sani ba cẽwa "Lalle ne wanda ya sãɓa wa Allah da ManzonSa, haƙĩƙa Yanã da wutar Jahannama, Yanã madawwami a cikinta? Waccan ita ce wulãkantãwa babba!"

9:64 Munãfukai sunã tsõron a saukar da wata sũra a kansu, wadda take bã su lãbãri ga abin da yake cikin zukãtansu. Ka ce: "Ku yi izgili. Lalle ne, Allah ne Mai fitai da abin da kuke tsõro."

9:65 Kuma lalle ne, idan ka tambaye,[1] su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"

9:66 "Kada ku kãwo wani uzuri, haƙĩƙa, kun kãfirta a bãyanĩmãninku. Idan Mun yãfe laifi ga wata ƙungiya daga gare ku, zã Mu azabta wata ƙungiya sabõda, lalle, sun kasance mãsu laifi."

9:67 Munãfukai maza da munãfukai mãtã, sãshensu[1] daga sãshe, sunã umurni da abin ƙi kuma sunã hani daga alhẽri. Kuma sunã damƙẽwar hannayensu. Sun mance Allah, sai Ya mantã da su. Lalle ne munãfukai sũ ne fãsiƙai.

9:68 Allah yã yi wa'adi ga munãfukai maza da munãfukai mãtã da kãfirai da wutar Jahannama, sunã madawwama a cikinta. Ita ce ma'ishiyarsu. Kuma Allah Yã la'ance su, kuma sunã da azãba zaunanniya.