>

Abubakar Mahmoud Gumi — 192

9:32 Sunã nufin su bice hasken Allah da bãkunãnsu. Kuma Allah Yanã ki, fãce dai Ya cika haskenSa, kuma kõ da kãfirai sun ƙi.

9:33 Shi ne wanda Ya aiko manzonSa da shiriya da addinin gaskiya, dõmin ya bayyanl shi a kan addini dukansa, kuma kõ dã mushirikai sun ƙi.

9:34 Yã waɗanda suka yi ĩmãni! Lalle ne mãsu yawa daga Ahbãr[1] da Ruhbãnãwa haƙĩƙa sunã cin dũkiyar mutãne da ƙarya, kuma sunã kangẽwa daga hanyar Allah. Kuma waɗanda suke taskacẽwar zĩnãriya da azurfa, kuma bã su ciyar da ita a cikin hanyar Allah, to, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.

9:35 A Rãnar da ake ƙõna shi a kanta a cikin wutar Jahannama, sai a yi lalas da ita ga gõshinansu da sãshinansu da bãyayyakinsu, (a ce musu): "Wannan ne abin da kuka taskace dõmin rãyukanku. To, ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã sanyãwa a taska."

9:36 Lallai ne ƙidãyayyun watanni a wurin Allah watã gõma shã biyu ne a cikin Littãfin[1] Allah, a Rãnar da Ya halicci sammai da ƙasa daga cikinsu akwai huɗu mãsu alfarma. Wannan ne addini madaidaici. Sabõda haka kada ku zãlunci kanku a cikinsu. Kuma ku yãƙi mushirikai gabã ɗaya, kamar yadda suke yãƙar ku gabã ɗaya. Kuma ku sani cẽwa lallai ne Allah Yanã tãre da mãsu taƙawa.