Abubakar Mahmoud Gumi — 18
2:113 Kuma Yahũdãwa suka ce: "Nasãra ba su zamana a kan kõme ba,"[1] kuma Nasãra suka ce: "Yahũdãwa ba su zamana a kan kõmeba," alhãli kuwa su, suna karãtun Littãfi. Kamar wancan ne waɗanda ba su sani ba suka faɗa, kamar maganarsu sabõda haka Allah ne ke yin hukunci a tsakãninsu a Rãnar ¡iyãma, a cikin abin da suka kasance suna sãɓawa jũna a cikinsa.
2:114 Kuma wãne ne mafi zãlunci[1] daga wanda ya hana masallãtan Allah, dõmin kada a ambaci sunanSa a cikinsu, sai kuma ya yi aiki ga rushe su? Waɗannan bã ya kasancẽwa a gare su su shigẽ su fãce suna mãsu tsõro. Suna da, a cikin duniya wani wulãkanci, kuma suna da, a cikin Lãhira, Azãba mai girma.
2:115 Kuma Allah ɗai yake da gabas da yamma sabõda haka, inda duk aka jũyar da ku, to, a can fuskar Allah take. Lalle ne, Allah Mawadãci ne, Mai ilmi.
2:116 Kuma suka ce: "Allah Yã riƙi[1] ɗã." Tsarki yã tabbata a gare Shi! A'a, Shi ne da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, dukansu, a gare Shi, mãsu ƙanƙan da kai ne.
2:117 Mai kyautata halittar sammai da ƙasa, kuma idan Ya hukunta wani al'amari, sai kawai Ya ce masa: "Kasance." Sai ya yi ta kasancewa.
2:118 Kuma waɗanda bã su da sani suka ce: "Don me Allah bã Ya yi mana magana, ko wata ãyã ta zo mana?"[1] Kamar wancan ne waɗanda suke a gabãninsu suka faɗa, kamar maganarsu. zukãtansu sun yi kamã da jũna. Lalle ne, Mun bayyana ãyõyi ga mutãne masu sakankancewa.
2:119 Lalle ne Mun aike ka da gaskiya, kana mai bãyar da bishãra, kuma mai gargaɗi, kuma bã zã a tambaye ka ba, game da abõkan Wuta.