>

Abubakar Mahmoud Gumi — 174

7:179 Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta sabõda Jahannama, mãsu yawa daga aljannu da mutãne, sunã da zukãta, ba su fahimta da su, kuma sunã da idãnu, bã su gani da su, kuma sunã da kunnuwa, ba su ji da su; waɗancan kamar bisãshe suke. Ã'a, sũ ne mafi ɓacẽwa; Waɗancan sũ ne gafalallu.

7:180 Kuma Allah Yanã da sũnãye mãsu kyau.[1] Sai ku rõƙe shi da su, kuma ku bar waɗanda suke yin ilhãdi a cikin sũnãyenSa: zã a sãka musu abin da suka kasance sunã aikatãwa.

7:181 Kuma daga waɗanda Muka halitta akwai wata al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma, da ita suke yin ãdalci.

7:182 Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu, zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba.

7:183 Kuma Inã yi musu jinkiri, lalle ne kaidĩNa, mai ƙarfi ne.

7:184 Shin, ba su yi tunĩni ba, cẽwa bãbu wata hauka ga ma'abucinsu?[1] shĩ bai zama ba fãce mai gargaɗi mai bayyanãwa.

7:185 Shin, ba su yi dũbi ba a cikin mulkin sammai da ƙasa, da kuma abin da Allah Ya halitta daga kõme, kuma akwai tsammãni kasancewar ajalinsu, haƙĩƙa, ya kusanta? To, da wane lãbãri a bãyansa suke yin ĩmãni?

7:186 Wanda Allah Ya ɓatar to bãbu mai shiryarwa a gare shi: kuma Yanã barin su, a cikin ɓatarsu sunã ɗimuwa.

7:187 Sunã tambayar ka[1] daga Sa'a, a yaushe tabbatarta take? Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Ubangijina yake. Bãbu mai bayyana ta ga lõkacinta fãce shĩ Tã yi nauyi a cikin sammai da ƙasa. Bã zã ta zo muku ba fãce kwatsam." sunã tambayar ka, kamar kai masani ne gare ta. Ka ce: "Abin sani kawai, saninta a wurin Allah yake, kuma amma mafi yawan mutãne bã su sani."