>

Abubakar Mahmoud Gumi — 171

7:160 Kuma Muka yayyanka su sibɗi gõma shã biyu, al'ummai. Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã a lõkacin da mutãnensasuka nẽme shi, ga shãyarwa, cẽwa: "Ka dõki dũtsen[1] da sandarka."Sai marmaro gõma shã biyu suka ɓuɓɓuga daga gare shi: Lalle ne kõwaɗanne mutãne sun san mashãyarsu. Kuma Muka saukar da darɓa da tantabaru a kansu."Ku ci daga mãsu dãɗin abin da Muka azurta ku."Kuma ba su zãluncẽ Mu ba; kuma amma rãyukansu suke zãlunta.

7:161 Kuma a lõkacin da aka ce masu: "Ku zauna ga wannan alƙarya[1], kuma ku ci daga gare ta, inda kuka so, kuma ku ce: 'Saryarwa,' kuma ku shiga kõfa kuna mãsu sujada; Mu gãfarta muku laifuffukanku, kuma zã Mu ɗãra wa mãsu kyautatãwa."

7:162 Sai waɗanda suka yi zãlunci daga gare su, suka musanya magana[1] watar wadda aka ce musu, sai Muka aika azãba a kansu, daga sama, sabõda abin da suka kasance sunã yi na zãlunci.

7:163 Kuma ka tambaye su daga alƙarya wadda ta kasance kusa ga tẽku, a lõkacin da suke ƙẽtare haddi a cikin Asabar, a lõkacin da kĩfãyensu, suke je musu a rãnar Asabar[1] ɗinsu jẽre. Kuma a rãnar da ba su yi Asabar ba, bã su zuwa gare su; Kamar wancan ne Muke jarraba su da abin da suka kasance sunã yi na fãsiƙanci.