>

Abubakar Mahmoud Gumi — 170

7:156 "Kuma Ka rubũta mana alhẽri a cikin wannan dũniya, kuma a cikin Lãhira. Lalle ne mũ, mun tũba zuwa gare Ka." Ya ce: "AzãbaTa Inã sãmu, da ita, wanda Nike so, kuma rahamaTa, ta yalwaci dukan kõme. Sa'an nan zã Ni rubũta ta ga waɗanda suke yin taƙawa, kuma sunã bãyar da zakka, da waɗanda suke, game da ãyõyin Mu mũminai ne."

7:157 "Waɗanda suke sunã bin Manzo[1], Annabi, Ummiyyi wanda suke sãmun sa rubũce a wurinsu, a cikin Attaura da Linjĩla.yanã umurnin su da alhẽri, kuma yana hana su daga barin abin da bã a so; kuma yana halatta musu abũ- buwa masu dadi, kuma yana haramtarwar mũnana a kansu. Kuma yanã kãyar da nauyinsu daga barinsu, da ƙuƙummai waɗannan da suka kasance a kansu. To, wa- ɗanda suka yi ĩmãni da shi kuma suka ƙarfafa shi, kuma suka tai- make shi, kuma suka bi haske wan- da aka saukar tãre da shi, waɗan- nan ne mãsu cin nasara.

7:158 Ka ce: "Yã kũ mutãne![1] Lalle ne nĩ manzon Allah nezuwa gare ku, gabã ɗaya. (Allah) Wanda Yake Shĩ ne da mulkin sammai da ƙasa; Bãbu wani abin bautawa fãce Shi, Yanã rãyarwa, kuma Yanã matarwa, sai ku yi ĩmãni daAllah da ManzonSa, Annabi, Ummiyyi, wanda yake yin ĩmãni da Allah da kalmominSa; ku bĩ shi, tsammãninku, kunã shiryuwa."

7:159 Kuma daga mutãnen[1] Mũsã akwai al'umma, sunã shiryarwa da gaskiya, kuma da ita suke yin ãdalci.