>

Abubakar Mahmoud Gumi — 164

7:105 "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni."

7:106 Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."

7:107 Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyanan ne!

7:108 Kuma ya fizge hannun sa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!

7:109 Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."

7:110 " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"

7:111 Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa.

7:112 "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi."

7:113 Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"

7:114 Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."

7:115 Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?"

7:116 Ya ce: "Ku jẽfa." To a õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."

7:117 Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!

7:118 Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.

7:119 Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.

7:120 Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada.