Abubakar Mahmoud Gumi — 163
7:96 Kuma dã lalle mutãnen alƙaryu sun yi ĩmãni kuma suka yi taƙawa dã haƙĩƙa Mun bũɗe albarkõki a kansu daga sama da ƙasa, kuma amma sun ƙaryata, don haka Muka kãma su da abin da suka kasance sunã tãrãwa.
7:97 Shin, mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbar Mu ta jẽ musu da dare, alhãli kuwa sunã barci?
7:98 Kõ kuwa mutãnen alƙaryu sun amince wa azãbarMu ta jẽ musu da hantsi, alhãli kuwa sunã wãsa?
7:99 Shin fa, sun amince wa makarun Allah? To, bãbu mai amince wa makarun Allah fãce mutãne mãsu hasãra!
7:100 Shin, kuma bai shiryar da waɗanda suke gãdon ƙasa ba daga bãyan mutãnenta cẽwa da Munã so, dã Mun sãme su da zunubansu, kuma Mu rufe a kan zukãtansu, sai su zama bã su ji?
7:101 Waɗancan alƙaryu Munã gaya maka daga lãbãransu, kuma lalle ne, haƙĩƙa manzanninMu sun jẽ musu da hujjõji bayyanannnu; to, ba su kasance sunã yin ĩmãnida abin da suka ƙaryata daga gabãni ba. Kamar wancan ne Allah Yake rufẽwa a kan zukãtan kãfirai.
7:102 Kuma ba Mu sãmi wani alkawari ba ga mafi yawansu, kuma lalle ne, Mun sãmi mafi yawansu, haƙĩƙa, fãsiƙai.
7:103 Sa'an nan kuma Mun aika Musa,[1] daga bãyansu, da ãyõyinMu zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka yi zãlunci game da su. To, dũbi yadda ãƙibar maɓarnata take.
7:104 Kuma Musa ya ce: "Ya Fir'auna! Lalle ne nĩ, manzo ne daga Ubangijin halittu."