>

Abubakar Mahmoud Gumi — 136

6:69 Kuma babu wani abu daga hisãbinsu (mãsu kutsãwa a cikin ayõyin Allah (a kan mãsu taƙawa amma akwai tunãtarwa (a kansu), tsãmmãninsu (mãsu kutsawar) zã su yi taƙawa.

6:70 Kuma ka bar waɗanda suka riƙi addĩninsu abin wãsa[1] da wargi alhãli rãyuwar dũniya tã rũɗe su, kuma ka tunãtar game da shi (Alƙur'ãni): Kada a jẽfa raia cikin halaka sabõda abin da ya tsirfanta; ba shi da wani majiɓinci baicin Allah, kuma babu wani mai cẽto; kuma, kõ ya daidaita dukan fansa, ba zã a karɓa ba daga gare shi. Waɗancan ne aka yanke wa tsammãni sabõda abin da suka tsirfanta; sunã da wani abin shã daga ruwan zãfi, da wata azãba mai raɗaɗi, sabõda abin da suka kasance sunã yi na kãfirci.

6:71 Ka ce: "Shin, zã mu yi kiran abin da bã ya amfãninmu, baicin Allah, kuma bã ya cũtar damu, kuma a mayar da mu a kan dugãduganmu, a bayan Allah Yã shiryar da mu kamar wanda shaiɗãnu suka kãyar da shi a cikin ƙasa, yanã mai ɗĩmuwa, yanã da abõkaisunã kiran sa zuwa ga shiriya, 'Ka zo mana'"[1] Kace: "Lalle ne, shiriyar Allah ita ce shiriya. Kuma an umurce mu, mu sallama wa Ubangijin tãlikai."

6:72 "Kuma (an ce mana): Ku tsai da salla kuma ku bĩ shi (Allah) da taƙawa kuma Shi ne wanda Yake zuwa gare Shi ake tãra ku."

6:73 Kuma Shĩ ne wanda Ya halitta sammai da ƙasa da mulkinSa, kuma a Rãnar da Yake cẽwa: "Ka kasance," sai abu ya yi ta kasancẽwa. Maganar Sa ce gaskiya, kuma gare Shi mulki yake a Rãnar da ake bũsa a cikin ƙaho. Masanin fake da bayyane ne, Kuma Shi ne Mai hikima Masani.