>

Abubakar Mahmoud Gumi — 135

6:60 Kuma Shĩ ne wanda Yake karɓar[1] rãyukanku da dare, kuma Yanã sanin abin da kuka yãga da rãna, sa'an nan Yanã tãyar da ku a cikinsa, dõmin a hukunta ajali ambatacce sa'an nan kuma zuwa gare shi makõmarku take, sa'an nan kuma Ya ba ku lãbari da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.

6:61 Kuma Shĩ ne Mai rinjãya bisa ga bãyinSa, kuma Yanã aikan mãsu tsaro a kanku, har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayanku, sai manzannin Mu su karɓi ransa alhãli su ba su yin sakaci.

6:62 Sa'an nan kuma a mayar da su zuwa ga Allah Ubangjinsu na gaskiya. To! A gare shi hukunci yake, kuma Shi ne Mafi gaugãwar mãsu bincike.

6:63 Ka ce: "Wane ne Yake tsĩrar da ku daga duhũhuwan tududa ruwa, kunã kiran Sa bisa ga ƙanƙan da kai Kuma a ɓõye: 'Lalle ne idan Ka tsĩrar da mu daga wannan (masĩfa), haƙĩƙa, muna kasancẽwa daga mãsu gõdiya?'"

6:64 Ka ce: "Allah ne Yake tsĩrar da ku daga gare ta, kuma daga dukan baƙin ciki sa'an nan kuma ku, kunã yin shirki!"

6:65 Ka ce: "Shĩ ne Mai ĩko a kan Ya aika da wata azãba a kanku daga bisanku, kõ kuwa daga ƙarƙashin ƙafãfunku, kõ kuwa Ya gauraya ku ƙungiyõyi, kuma Ya ɗanɗanã wa sãshenku masĩfar sãshe." "Ka dũba yadda Muke sarrafa ãyõyi, tsammãninsu sunã fahimta!"

6:66 Kuma mutãnenka sun ƙaryata (ka) game da Shi, alhãli kuwa Shi ne gaskiya. Ka ce: "Nĩban zama wakĩli a kanku ba."

6:67 "Akwai matabbata ga dukan lãbãri, kuma zã ku sani."

6:68 Kuma idan kã ga waɗanda suke kũtsawa a cikin ãyõyinMu, to, ka bijire daga gare su, sai sun kũtsa a cikin wani lãbãri waninsa. Kuma imma dai shaiɗan lalle ya mantar da kai, to, kada ka zauna a bayan tunãwa tãre da mutãne azzãlumai.