>

Abubakar Mahmoud Gumi — 506

46:29 Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu[1] zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.

46:30 Suka ce: "Ya mutãnenmu! Lalle mũ, mun ji wani littãfi an saukar da shi a bãyãn Mũsã, mai gaskatãwa ga abin da ke a gaba da shi, yanã shiryarwa ga gaskiya da kuma zuwa ga hanya madaidaiciya.

46:31 "Yã mutãnenmu! Ku karɓa wa mai kiran Allah, kuma ku yi ĩmãni da Shi, Ya gãfarta muku daga zunubanku, kuma ya tserar da ku daga azãba mai raɗaɗi.

46:32 "Kuma wanda bai karɓa wa mai kiran Allah ba to bai zama mai buwãya a cikin ƙasa ba, kuma ba ya da waɗansu majiɓinta, baicin Shi. Waɗannnan sunã a cikin ɓata bayyananna."

46:33 Shin, kuma ba su gani ba cẽwa: "Lalle Allah, Wanda Yã halitta sammai da ƙasa kuma bai kãsa ga halittarsu ba, Mai ĩkon yi ne a kan rãyar da matattu?" Na'am, lalle Shi, Mai ĩkon yi ne a kan kõme.

46:34 Kuma rãnar da ake gittar da waɗanda suka kãfirta a kan wutã, (a ce musu) "Ashe, wannan bã gaskiya ba ne?" Su ce: "Na'am, gaskiya ne, mun rantse da Ubangijinmu!" Sai Ya ce, "To, ku ɗanɗani azãbar sabõda abin da kuka kasance kunã yi na kãfirci."

46:35 Sabõda haka, ka yi haƙuri kamar yadda mãsu ƙarfin niyya daga Manzanni suka yi haƙuri. Kuma kada ka yi musu gaggãwa. Kamar dai sũ, a rãnar da suke ganin (sakamako) abin da ake yi musu wa'adi ba su zauna ba, fãce sa'a guda daga yini. Iyarwa dai da Manzanci). Shin, akwai wanda za a halakar? (Bãbu), fãce mutãne fasiƙai.