>

Abubakar Mahmoud Gumi — 493

43:48 Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa.

43:49 Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne."

43:50 To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu.

43:51 Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba?"

43:52 "Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar?

43:53 "To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe?"

43:54 Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai.

43:55 Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.

43:56 Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe.

43:57 Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili.

43:58 Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.[1] Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma.

43:59 Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla.

43:60 Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa[1]