>

Abubakar Mahmoud Gumi — 590

84:25 Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.

85:1 Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara.

85:2 Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa,[1]

85:3 Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta[1] a cikinsa

85:4 An la'ani mutãnen rãmi.[1]

85:5 Wato wuta wadda aka hura.

85:6 A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune.

85:7 Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce.

85:8 Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa.

85:9 Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake.

85:10 Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara.

85:11 Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba.

85:12 Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai.

85:13 Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa).

85:14 Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya.

85:15 Mai Al'arshi mai girma

85:16 Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi.

85:17 Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka.

85:18 Fir'auna da samũdãwa?

85:19 Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa.

85:20 Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa).

85:21 Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma.

85:22 A cikin Allo tsararre.