Abubakar Mahmoud Gumi — 546
59:4 Wannan dõmin lalle su, sun sãɓa wa Allah, da ManzonSa alhãli kuwa wanda ya sãɓa wa Allah, to, lalle Allah, Mai tsananin uƙũba ne.
59:5 Abin da kuka sãre na dabĩniya, kõ kuka bar ta tsaye a kan asallanta, to da iznin Allah ne, kuma dõmin Ya wulãkanta fasiƙai,
59:6 Kuma abin da Allah Ya sanya ya zama ganĩma ga Manzon Sa, daga gare su, to, ba ku yi hari a kansa da dawãki ko rãƙuma ba amma Allah ne Ya rinjãyar da Manzannin Sa a kan wanda Yake so, kuma Allah Mai ĩkon yi ne a kan kõme.
59:7 Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga Manzon Sa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na Manzon Sa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya[1] (matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.
59:8 (Ku yi mãmãki) Ga matalauta mãsu hijira waɗanda aka fitar daga gidãjẽnsu da dũkiyõyinsu, sunã nẽman falala daga Allah da kuma yarda, kuma sunã taimakon Allah da Manzon Sa! Waɗannan sũ ne mãsu gaskiya.
59:9 Da waɗanda suka zaunar da gidãjensu (ga Musulunci) kuma (suka zãɓi) ĩmãni, a gabãnin zuwansu,[1] sunã son wanda ya yi hijira zuwa gare su, kuma bã su tunãnin wata bukãta a cikin ƙirãzansu daga abin da aka bai wa muhãjirĩna, kuma sunã fĩfĩta waɗansu a kan kãwunansu, kuma ko dã sunã da wata larũra. Wanda ya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo.